ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar dakarun ta na bada wannan labarin a jiya Lahadin.
Labarin ya kara da cewa bayan murkushe yunkurin ‘yan ta’addan, wasu daga cikinsu sun tsere, a yayinda wasu kuma suka fada hannun dakarun na Hashd.
Duk da cewa an kawo karshen ikon kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a arewa da kuma yammacin kasar Iraqi tun shekara ta 2017, amma har yanzun wasu ‘ya’yan kungiyar wadanda suke ta kai hare-hare a kasar nan da can, a duk fadin kasar, a duk lokacinda su ka sami damar yin hakan.
342/